Soyayya gamon jini: ‘Yar Indiya da auren dan Nigeria
– Wani dan Nigeriya mazaunin Lagos na shirin angwancewa da wata ‘yar india
– Hotunan shirye-shiryen bikin ya ja hankalin mutane a shafukan sada zumunta da muhawara a intanet
– ‘Yar indiya Farida ruwa biyu ce, za a sha shagalin biki na ba da dedewa ba
Ango Jimi Ogunlela na shirin tarewa da amaryarsa Farida wata ‘yar indiya wacce aka dade da yin baiko a ke kuma jiran ranar da za’a daura aure.
KU KARANTA KUMA: Aure ba zai hana ni yin fim ba – Rahma Sadau
‘Yar indiya Farida mai ruwa biyu ce, kuma tana da gidan burodi, ta kuma shahara da yin kek da sauran kayan kwalam da makulashe ga ‘yan birni a Lagos, yayin da mai shirin angwancewa Jimi, bayarbe ne mai sana’ar saye da sayarawa, da kuma zabar motocin alfarma ga masu hannu da shuni.
Farida da Jimi sun jima da sanin juna kafin daga baya sun amince da juna, da kuma batun daurin aure, nan ba da dadewa ba, a cewar bakin da baya karya, kuma bisa al’ada ta zamani, amarya da ango masu jiran rana, sun dauki hotunan albishir na jiran rana, kamar yadda kuke gani:
Jimi da Farida
Lallai soyayya gamon jini
The post Soyayya gamon jini: ‘Yar Indiya da auren dan Nigeria appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.