Rashawa ta ratsa dukkam ma’aikatun gwamnati- Osinbajo
– Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya jingina mawyacin halin da yan Najeriya ke ciki ga rashawa
– Yace yaki da rashawan wannan gwamnati zata taba kowani lungu da sako
Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya jingina mawyacin halin da yan Najeriya ke ciki ga rashawa, ya bayyana yadda rashawa ta ratsa dukkan ma’aikatun gwamnati.
Jaridar The Punch ta bada rahoton cewa mataimakin shugaban kasan wanda yayi Magana a Ado Ekiti wajen taro yaye daliban Jami’ar Afe Babalola y ace yaki da rashawa zai taba kowani sako.
KU KARANTA: Dalilan da yasa ba zamu daina jefa bama-bamai a dajin Sambibsa ba – Hukumar sojoji
Yace : “Ina girmama Afe Babalola saboda matsayarshi ga rashawa. A shekarar 2002, Babaloa yayi kokari wajen kafa hukumar ICPC inda ya sanar da kotu cewa rashawa itace babban matsalan wannan kasa.
Rashawa ta ratsa dukkan ma’aikatun gwamnati, ina nufin bangaren zantarwa, dokoki da shari’a.
Shi yasa wannan gwamnatin ta hannu wajen yaki da rashawa saboda idan muka kidukkan sassan kasa zai durkushe. Dole ne muyi gaggawa wajen kawo sauyi.”
Kana gwana Ayodele fyose yayi kira da gwamnatin tarayya domin gina filin jirgi a jihar. A jawabin sa, Osinbajo yace jihar Ekiti ta cancanci filin jirgin sama amma zai tattauna da shugaban kasa idan ya koma.
The post Rashawa ta ratsa dukkam ma’aikatun gwamnati- Osinbajo appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.