Yan bindiga sun sace Muhammad Madoki da matarsa
– An sace sheik Muhammad Madoki da matar sa a yayin da suke tafiya
– Malamin da ya kasance shugaban zakka da wakafi na jahar Sokoto
– Yan sanda sun fara binciken satar shi da akayi
Wasu yan bindiga da ba’a sani ba sun sace wani babban malami musulunci, Sheikh Muhammad Madoki kan babbar hanyar Abuja zuwa Kano.
BBC sun ruwaito cewa babban Malamin, da matar shi, da surukar shi, da matar kanin shi yan bindigan da ba’a sani ba suka sace su yayin da suke tafiya ranar Alhamis 20 ga watan Oktoba.
KU KARANTA KUMA: Hoton shugaba Buhari yana rawa da wata mace
Anyi rohoton sace babban Malamin Madoki ga yan sanda, Malamin ya kasance shugaban hukumar zakka da wakafi na jahar Sokoto, kuma har an fara binciken.
Donald Awunah wanda shine kakakin yan sanda na yankin yace ba’a bashi wani bayani ba kan lamarin. “Banda wani bayani kan lamarin, ba’a fada man komai ba, amma Kila zuwa gobe za’a man bayani.”
Sai dai har yanzu sojojin Najeriya suna nan suna kokarin kawar da masu satar mutane da yan tada kayar baya, inda a cikin lamarin an kashe yan ta’adda guda 4 a Zamfara.
The post Yan bindiga sun sace Muhammad Madoki da matarsa appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.