Rayuwa a masarautar Gbaramatu
Daga Edita: Sojojin Najeriya su sha kai hare-hare a masarautar Gbaramatu yayin da suke farautar tsohon jagorar tsagerun Neja Delta Government Ekpemupolo wanda aka fi sani da Tompolo, tare da sauran tsagerun da ke barna a yankin.
Donald O.O Ejewentotor Esq, wani makarancin NAIJ.com ya aiko mana da wakar da ya rera game da rayuwa a masarautar Gbaramatu tun da hare-haren tsagerun ya karu
Rayuwa a masarautar Gbaramatu (daga Donald O.O Ejewentotor Esq)
A masarautar Gbaramatu ba bata lokaci
An gama zaman lafiya
Maza, mata kowa cikin rudani
Ban san asalin wannan ketar ba
Amma a Gbaramatu kowa sai kuka
A Gbaramatu, da an ganka sai kamu
Kamar tsuntsaye, ga gudu ba wurin zuwa
Duk a watse karkashin wata da hasken rana
Ni kaina ban san dalilin binciken ba
Dalilin zama Neja Delta, Gbaramatu farin cikin Nazi
Kamar dangin Wiwa, maras laifi ke shan wahala
Ba’a ragama ko na goye
Ba kamar mulki ba, gudu ne abin yi
Tsaffi da yara na mutuwa domin yunwa
Kasar su ta gado ta gurbanta
Abin da ya rage ma kasar sai kifaye masu guba
Dole ‘yan Neja Delta su hada kai suyi yaki
The post Rayuwa a masarautar Gbaramatu appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.