Shugaba Buhari ya dawo Najeriya
– Shugaba Buhari ya dawo Najeriya bayan tafiyar kwanan 3 da yayi zuwa kasar Jamus
– Shugaban kuma ya mayar da martani ga matarsa a Jamus
Shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da kansilar kasar Jamus
Shugaba Buhari ya dawo ne a ranan Asabar, 18 ga watan Oktoba bayan wata ziyara da ya kai kasar jamus inda ya hadu da shugabar Jamus, Angela Merkel da kuma shugaban kasan Joachim Gauck a Berlin.
Shugabannin kasan sun tattauna ne akan yaki ga boko haram dakuma matsalan yan gudun hijra da tallafin da ake musu ,tare da kuma wasu al’amura masu muhimmanci.
KU KARANTA: Buhari ya ziyarci babban hafsan soja a asibitin Berlin
Zaku tuna cewa shugaba Buhari ya mayar da martani ga matarsa, Aisha Buhari, akan maganan da tayi a Ingila ,. Yai martanin ne a waa hira da yan jarida tare da Angela merkel a kasar Jamus.
Yace : ban san ko mata ta yar wace jam’iyya bace, amma mai girki n ace kuma yar daki na, kuma mai dakina.
The post Shugaba Buhari ya dawo Najeriya appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.