Attajirin nan na Kasar Japan ya cika alkawarin sa ga yan kwallon Najeriya
– Kungiyar Dream Team ta Najeriya ta samu kyautar kudi daga wani kasaurgumin Attajiri na Kasar Japan.
– Kocin Kungiyar Samson Siasia da kuma Kyaftin din ta John Mikel Obi sun samu kyautar kudi har dala $200,000 da kuma $190,000.
Kyaun alkawari, cikawa: Hamshakin mai kudin nan na Kasar Japan ya cika alkawarin da ya dauka ga ‘yan wasan kwallon kafar Najeriya a Gasar Olympics.
Katsuya Takasu, likitan nan mai kudi na Kasar Japan ya cika alkawarin da ya dauka ga ‘yan Kungiyar Dream Team ta Najeriya. Takasu yayi alkawarin ba ‘yan wasan Najeriya kyautar kudi idan har suka ci kyautar gwal, ko zinari ko kuma tagulla a Gasar Olympics.
Kocin Kungiyar Kasar Samson Siasia ya samu kyautar dala 200,000 yayin da kuma Kyaftin din Kungiyar, John Mikel Obi ya tashi da Dala 190,000 shi kuma. Kungiyar kwallon ta Najeriya dai ta doke Kasar Honduras ne a Gasar na Olympics, hakan ya sa Najeriya ta samu lashe kyautar Tagulla a Gasar da ake yi a Birnin RIO.
KU KARANTA: MARTANIN YAN NAJERIYA BAYAN JAMUS TA DOKE NAJERIYA
Sai dai ana samun labari cewa, Kungiyar kwallon kafa ta Kasar NFF, ta na kokarin yin awon gaba da wannan kyauta. Wani mai harsashe a harkar kwallon kafa kuma tsohon golana Super Eagles ya bayyana wannan labari dai. Ana cewa Attajirin ya raba kudin ne ga ‘yan wasan kai tsaye bayan nasarar da suka samu a dakin otel din na su.
Idah Peterside din ne dai ya bayyana wannan labari ta shafin san a twitter, inda ya rubuta cewa: “Abu yayi kyau! An mika takardun kudi guda biyu ga Koci Samson Siasia da kuma Kyaftin Mikel Obi”. Haka ma wani Oluwashina Olakeji ya kara tabbatar da wannan labari tare da wasau hotuna. Attajirin dai ya bada kyautar Dala $390,000 ke nan ga Yan Kungiyar Dream Team din.
The post Attajirin nan na Kasar Japan ya cika alkawarin sa ga yan kwallon Najeriya appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.