Lauyoyi sun gargadi Buhari a kan bincikan Jonathan kan ND Avengers
-Zargin cewa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan yana daga cikin wadanda ke daukar nauyin yan bindiga a Najeriya ya ci gaba da janyo cece-kuce
-Lauyoyin kasar sun hada muryoyinsu gurin shawara sun kuma fada wa shugaban kasa Muhammadu Buhari abunda zaiyi game da zargin
-Sun kuma gargadi Buhari kan wulakantar da tsohon shugaban kasan a matsayin gudanar da bincike ba tare da hujja ba
Wasu Lauyoyin Najeriya sun gargadi shugaban Kasa Muhammadu Buhari game da shirin da aka ruwaito da cewa zai binciki tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan kan zargin da ake masa na cewa shi ke daukar nauyin yan bindigan Niger Delta Avengers.
shugaban kasa Buhari da tsohon shugaban kasa Goodluck
Kungiyar Movement for the Emancipation of the Niger Delta (MEND) sun ambaci Jonathan a matsayin daya daga cikin masu daukar nauyin kungiyar yan ta’addan dake ta faman saka bam a bututunan man gwamnati a fadin yankin Niger Delta suka kuma yi barazanar samar da yancin kai a ranar 1 ga watan Oktoba.
Tsohon shugaban kasar a bangarensa ya karyata zargin tare da nuna wadanda ke bakin ciki ga ci gaban da ya samu a kasashen waje a matsayin masu danganta shi da yan bindigan.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Femi Falana, daya daga cikin Lauyoyin da sukayi Magana kan al’amarin ya gargadi gwamnatin tarayya da ta binciki Jonathan idan tana da kwakwaran hujja dake nuni ga cewa lallai yana da hannu a ciki.
KU KARANTA KUMA: Gwamnatin tarayya ta zuba biliyoyin naira cikin tattalin arziki
Falana, wani Lauyan kare hakkin dan adam dake zaune a jihar Lagas, yace dole ne ayi takatsantsan da zargi irin wannan.
A bangarensa, Auwalu Hamisu Yadudu, wani Farfesan shari’a, yace koda dai babu laifi a bincikan Jonathan, dole hujjar ta zama na hakika.
A nashi shawaran, wani babban Lauya, Abeny Mohammed, yace: “wannan bashi bane abunda kasar ke bukata ba a yanzu. Wannan kasar ba kasar-jiha bace, muna rusa zaman lafiyar ta ne kawai.”
The post Lauyoyi sun gargadi Buhari a kan bincikan Jonathan kan ND Avengers appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.