Oshiomole yayi ba’a ga dan takarar PDP Ize-Iyamu
– Zaben 10 ga watan Satumba zai zama ma jam’iyyar APC abu mai sauki kamar cin tuwo inji Gwamna Adams Oshiomole na Edo.
– Yace jam’iyyar APC kamar ta ci zabe ta gama ne ganin PDP ta tsaida Osagie Ize-Iyamu a matsayin dan takarar ta, Jaridar Vanguard ta rahoto wannan labari.
– Oshiomole ya bada wannan sanarwar a ranar Litinin, 20 na watan Yuni, yayin da ya hadu da wasu wakilan jam’iyyar ta APC.
Oshiomole yayi ba’a ga dan takarar jam’iyyar PDP Osagie Ize-Iyamu
Oshiomole yake cewa: “Nayi matukar murna da Ize-Iyamu ya lashe tikitin PDP, domin kuwa babu wanda zai yi ma Obaseki saukin karawa kamar sa. Yayin da mu zamu nuna ma ‘yan jihar Edo aikin da muka yi masu wajen kamfe, shi kuwa (dan takarar PDP) zai ta faman wasan kura da hukumar EFCC da kuma zaman kotu saboda abin da ya aikata a baya a wannan Jihar.”
“Obaseki mutum ne mai kwakwalwa, shine kusa wajen nasarar wannan gwamnati, ina mai tabbatar wa mutane zai yi abun kwarai idan aka zabe sa. Babu shakka Zaku yi alfahari da Obaseki.” Cewar gwamna Adams Oshiomole.
NAIJ.com za ta iya tuna cewa wancan makon da ya wuce ne hukumar yaki da cin hanci da rashawa a kasar (EFCC) ta kama Ize-Iyamu jim kadan bayan ya halarci taron tantance dan takarar jam’iyyar PDP a Birnin Benin, babban Birnin Jihar ta Edo. An dai tsare Ize-Iyamu wanda Fasto ne a babban cocin ‘RCCG’ game da zargin cin kudin makaman da aka raba wajen yakin neman zabe a shekarar 2015. Sai dai tuni kwamitin yakin neman cin zaben Fasto Osagie Ize-Iyamu ta musanta wannan zargi, inda tace ba gaskiya bane.
The post Oshiomole yayi ba’a ga dan takarar PDP Ize-Iyamu appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers.