Brazil ta nada sabon koci bayan ta kori Dunga
– Brazil ta nada sabon koci bayan ta kori Dunga
– Brazil ta kori Dunga, ta maye gurbin sa da Tite
– Kocin kulob din Corinthians Tite ne zai maye gurbin Dunga.
– Tun a zagayen farko na gasar nahiyar Amurkar a ka fatattaki Kasar Brazil.
Kungiyar Kwallon Kafar Kasar (CBF) ta sanar da nadin Tite, kocin kulob din Corinthians a matsayin mai horar da ‘yan wasan kwallon Kasar bayan an salami Dunga. An sallami Dunga ne daga aikin bayan a kori Kasar Brazil din daga gasar Copa America da ake yi wannan shekarar. Kafar CNN ta yada cewa maganar nada Tite tamkar anyi-an gama, kawai albashi ya rage a gama tattaunawa. Asalin sunan Tite din dai shine Adenor Bacchi.
Tite ya taba cin gasar gidan Kasar na Seria A har sau biyu, kuma ya taba cin kofin Copa Libertadores, ya ma taba lashe gasar kulobs din kwallon kafan duniya yayin da yake tsare da kungiyar Sao Paulo ta kasar Brazil din.
Tite ya lallasa Kungiyar Sao Paulo, mai adawa da ci 6-1 a gasar Seria A ta kasar, inda ya samu zama Gwarzon Koci a Shekarar.
The post Brazil ta nada sabon koci bayan ta kori Dunga appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers.