Arsenal ma na so ta sayi Romelu Lukaku daga Everton
– Arsenal ma na so ta saye Lukaku daga Everton.
– Kulob din Arsenal na duba yiwuwar sayen dan wasa Romelu Lukaku.
– Kungiyar kwallon Arsenal din ta fasa sayen Jamie Vardy na Kungiyar Leicester City.
– Dillalin dan wasan yace Lukakun na iya zaman sa gidan wasa na Goodison Park
Kulob din Arsenal sun bi jerin sahun masu son sayen dan wasan Everton Romelu Lukaku, wanda a matse yake da ya bar kulob din nasa bayan kammala gasar EURO 2016.
Kungiyar Arsenal din sun hakura da sayen Jamie Vardy bayan da Koci Arsene Wenger ya sanar da cewa dan wasan gaban na Leicester zai yi zaman sa a kulob din sa. Haka dai Dillalin dan wasan ya bayyana cewa Lukaku na iya yin zaman sa a Everton din ganin Ronald Koeman ya dawo kulob din da horarwa daga kulob din Southampton.
Mino Riola wanda shine dillalin Lukaku yake cewa: “Everton ba kudi take nema ba, yanzu cin kofi ake bukata. Abubuwa sun canza a kulob din. Idan dai har zai bar kulob din Everton, to zai zama shine abin da ya fi dacewa yayi”
Kungiyoyi da dama na neman dan wasan gaba, Romelu Lukaku wanda ya zura kwallaye har 25 a raga a gasar shekarar da ta gabata.
The post Arsenal ma na so ta sayi Romelu Lukaku daga Everton appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers.