Ambode ya sanya hannu ga wata yarjejeniya da Dubai
– Ambode ya tafka hannun wata muhimmiyar yarjejeniya da Dubai.
– Legas ta sa hannun kan wata muhimmiyyar yarjejeniyar gina wani birni da Dubai.
– Amobode ya tafka hannu kan wata yarjejeniyar biliyoyin dalar Amurka
– Ambode yace wannan gagarumin aiki zai sama wa mutanen gari aikin yi.
Gwamnan Legas Mista Akinwumi Ambode (karshe daga gefen hagu) tare da Mataimakin Shugaban Kasar UAE Mr. Ahmad Bin Hayat (Karshe dagaa dama) da kuma Kwamishinan Shari’a na Jihar Mr. Adeniji Kazeem (Daga dama) tare da Shugaban Kamfanin Smart City Dubai Mr. Jabber Bin Hafez (Daga Hagu) a Benayen Emirates, Birinin Dubai ranara 20 ga watan Yuni, wajen sa-hannun yarjejeniyar.
Gwamnatin Jihar Legas ta sa hannun da Dubai wajen gina wani birni a garin Legas din, wannan dai shine karo na farko a tarihin Afrika da za a gina irin wannan Birni na ‘Smart City’. An tafka wannnan yarjejeniyar ne a Emirate Towers da ke Birnin Dubai. Atoni-Janar kuma Kwamishinan Shari’ar Jihar Mr. Adeniji Kazeem da kuma Shugaban kamfanin na Smart City Dubai LLC, Mr. Jabber Bin Hafez suka sa hannu wajen wannan yarjejeniya.
Gwamnan Jihar ta Legas Akinwumi Ambode da kuma Mataimakin Shugaban Kasar UAE din, kuma Shugaban Kamfanin Dubai Holdings suna wajen kulla wannan yarjejeniyar da za ta sa Legas ta zama ta farko a kaf Nahiyar Afrika da ta gina irin wannan birni,
Gwamnan Legas, Ambode ya sanar ta bakin kwamishinan watsa labaran Jihar, Mr. Steve Ayorinde, cewa wannan yarjejejiniyar za ta kawo ma Jihar biliyoyin dalolin kudi, a kuma samar da gidaje da dama a Jihar. Haka kuma dai wannan yarejejeniya za ta samar da aikin yi da dama, kuma za a canza fuskar Ibeju zuwa Lekki da ma Jihar din dai gaba daya. Ambode yake bayyana cewa wannan duk yunkuri ne na ganin an kara gyara Jihar Legas din. Yake kara bayanin cewa kamar yadda ake da irin wadannan birane Smart City a biranen duniya kamar su Malta (Kasar Dubai) da Koci (Kasar India), haka za a samu a birnin Legas, wanda zai zama na farko a tarihin Afrika.
Gwamnan Legas, Mr. Akinwunmi tare da Mataimakin Shugaban Kasar United Arab Emirate (UAE) Mr. Ahmad Bin Byat (duk a sama); da kuma Shugaban Smart City Dubai LLC, Mr. Jabber Bin Hafez tare da Kwamishinan Shari’a na Legas, Mr. Adeniji Kazeem (Da takardu a Kasa) wajen tafka hannu a yarjejeniyar tsakanin Legas da Dubai a Emirate Towers, Dubai, ranar Litinin 20 ga watan Yuni, 2016.
The post Ambode ya sanya hannu ga wata yarjejeniya da Dubai appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers.