Abinda ya faru a kotun CCT a yau
– An dakatar da shari’ar Senata Bukola Saraki a kotun CCT
– Saraki ya sake neman Danladi Umar ya janye daga shari’ar sa.
– Shugaban majalisan dattawa yayi ikirarin cewa Danladi Umar na da kara a EFCC, saboda haka ba shi da hakkin yi masa shari’a.
Bukola Saraki kenan a kotun cct
Kotun CCT dake zaune a Abuja, babban birnin tarayya ta sake dakatar da shari’ar Bukola Saraki zuwa ranar laraba 13 ga watan yuli. An yanken shawaran hakane yayinda alkalin kotun ya ce zai yi tafiya gobe , laraba 22 ga yuni,saboda haka ba zai samu daman zuwa ba. A cikin kotun Shari’ar , lauyoyi sun yi jayayya akan karar da Shugaban majalisa dattawa, Bukola Saraki ya shigar na cewan Alkalin kotun ya janye daga shari’ar sa.
Saraki ya fadi hakan ta dalilin cewa Danladi Umar na da kashi a gindi a wurin hukumar hana al mundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zaman kasa ,wato EFCC.
Amma ranar Alhamis, 21 ga watan afrilu, Danladi Umar yayi watsi da karar shugaban majalisa dattawan ya shigar na cewan ya janye daga karar.
KU KARANTA: Yanzu-yanzu: An dakatar da shari’ar Saraki da Ekewremadu
A cikin karar, Saraki ya tuhumce danladi Umar da bin son kai.
Bayan haka, Saraki ya kara shigar da wata kara a ranar laraba 15 ga watan yuni ta Danladi Umar ya janye fa.shugaban Lauyoyin Senata Bukola Saraki, Kanu Agabi ne ya shigar da karar. Amma dai an dakatar da karan zuwa ranar 21 ga yuli.
Saraki na gurfana a kotun CCT tun 22 ga satumba 2015 akan laifuffuka 16 na rashawa. Banda hakan, EFCC na tuhumar da sa hannu a cikin aikin yan jabun da akayi na chanja dokokin majalisar dattawa ba bisa doka ba.
The post Abinda ya faru a kotun CCT a yau appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers.