An tabbatar da tafiyar Kocin PSG Lauren Blanc
– An tabbatar da tafiyar Kocin PSG
– Kulob din PSG za ta kori kocin ta Laurent Blanc.
– Za a maye gurbin nasa da Unai Emery.
– Dillalin Blanc din ya tabbatar da jita-jitar.
Dillalin kocin na PSG ya sanar da cewa Laurent Blanc din zai bar kungiyar kwallon kafar ta Faransa. A wannan shekarar dai kulob din PSG din ta lashe kofunan Trophee des Champions, the Coupe de la Liga, the Coupe de France da kuma Ligue 1, sai dai koren ta da aka yi daga gasar nahiyar turai na Champions league bai zo da dadi ba.
Da aka tambayi mai kungiyar kwallon PSG Nasser Al-Khelaifi ko Blanc zai ci gaba a matsayin manajan kungiyar ta PSG sai yake mai cewa: “Ba zanyi magana ba kan wasu abubuwa, Wasu abubuwa za su faru. Za a shiga wanin sabon zamani, za ku gani. Amma dai idan muka ci gaba a haka a dukkan mataki, to babu inda za mu je.” Yake (Khelaifi) cewa: “Awa biyu kafin a take wasan mu da Manchester City nake fada ma wani daga cikin ma’aikatana, ba za mu ci wasa ba. Ban ga alamun hakan ba, ko kadan na san ba za muyi nasara ba. Haka aka doke mu da ci 3-2”
Na goya masa baya har shekaru 3 yanzu, dole kuma yanzu muga abin da zai faru nan gaba. Dole mu gina kulob din nan, mu kara karfi domin a goga da mu cikin turai. Inji Al-Khelaifi.
Rahotanni sun nuna cewa kulob din ta kammala shirin dauko hayar mai horar da ‘yan kungiyar Sevilla ta kasar Spain, Umai Emery domin ya maye gurbin Lauren Blanc din. A da kungiyar kwallon ta PSG tayi niyyar dauko kocin kulob din Atheletico Madrid watau Diego Simeone ya canji Blanc, sai dai ta ga kamar hakar ba za ta ci ma ruwa ba. Kafin karshen wannan makon kungiyar PSG din da Laurent Blanc za su raba jiha, inji wakilin Blanc din Jean Pierre Bernes.
The post An tabbatar da tafiyar Kocin PSG Lauren Blanc appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers.