Mu zamu zabi shugaban kwamitin amintattu– Gwamnonin APC
– Rikicin da ke faruwa a cikin jam’iyyar APC ta dau sabon salo
– Gwamnonin jam’iyyar sunce yarde cewan sune zasu zabi shugabannin jam’iyyar
Hayaniyan da ke faruwa tsakanin shugaban APC, Chief John Odigie-Oyegun,da babban jigon APC, Asiwaju Ahmed Tinubu ta dau sabon salo.
Gwamnonin jam’iyyar APC sun yarde cewan zasuyi amfani da wannan daman su kwace akala shugabncin jam’iyyar.
KU KARANTA: Darajar Naira ta yi mummunar faduwa saboda wannan dalilin (Karanta)
Wannan mai ruwa da tsaki a jam’iyyar ya fada ma NAIJ.com cewa wutan da tashin tsakanin Oyegun da Tinubu na daga cikin abubuwan da gwamnonin APC suka tattauna a ganawarsu.
Jigon jam’iyyar wanda aka sakaye sunansa saboda ba’a yarda yayi Magana akan abubuwn da jam’iyya a waje bayace gwamnonin na son suyi amfani da kujeran shugaban kwamitin amintattu domin kwace jam’iyyar.
Yace: “Wani gwamna daga yankin arewa maso yamma ne ya kawo Magana kuma sauran suka ki amincewa, kana sai suka fara zana yadda zasu wace jam’iyyar ta hanyar dauke kujeran shugaban kwamitin amintattu.”
ku biyo mu a shafinmu na Tuwita: @naijcomhausa
The post Mu zamu zabi shugaban kwamitin amintattu– Gwamnonin APC appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.