Gwamnatin Najeriya ta yi amai-ta-lashe (Karanta)
– Gwamnatin Najeriya na shirin ganawa da shugabanin kabilun Naija Delta da kuma tsagerun dake fasa bututun mai a makon gobe, domin ganin an kawo karshen tashin hankalin da ake samu a yankin
– Kamfanin dillancin labarai na Reuters, ya ruwaito majiyar gwamnatin kasar na cewa za’a gudanar da taron ne ranar litinin mai zuwa a Abuja
Ana saran shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da Ministan mai Ibe Kachikwu su jagoranci taron.
Gwamnatin Najeriya ta shafe watanni tana kokarin kawo karshen tashin hankalin da ke aukuwa a yankin Niger Delta, sai dai har yanzu bata samu nasarar cimma hakan ba.
KU KARANTA: Rundunar sojoji ta kama wani sojan bogi
Tsagerun Niger Delta Avengers, wadanda tun a farkon shekara ta 2016 suke daukar alhakin fasa tarin bututun mai, sun bayyana dakatar da kai hari a watan Agusta, sai dai kuma a watan Satumban da ya gabata suka kara kai wani harin na lalata butun mai.
A wani labarin kuma, Gwamnonin jam’iyyar APC mai mulkin Nigeria sun nemi Shugaba Muhammadu Buhari ya yi adalci da daidaito wurin nada jakadun kasashen waje.
A ranar Alhamis ne shugaban ya mika sunayen mutum 46 zuwa ga majalisar dattawan kasar domin ta tantance su don zama jakadun kasar a kasashen waje.
Sai dai batun ya tayar da hargitsi a fagen siyasar kasar, inda wasu da dama suke korafin cewa ba a zabo wadanda suka yi wa jam’iyyar hidima ba.
A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa
The post Gwamnatin Najeriya ta yi amai-ta-lashe (Karanta) appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.