Kalli abincin da Sojojin Najeriya ke korafin cewa sun gaji da shi (hotuna)
Idan mutun yayi nisa da gida yana kuma bauta wa kasarsa, babu shakka zai so dandana gida ko da kuwa akalla a cikin abincin da ake ciyar dashi.
Vitalis Kawunda Lee Odikamnoro tare da wasu sojoji
Sojojin Najeriya, wadanda ke yaki da yan ta’adda, a kullun suna kokari don ganin cewa mun kasance cikin tsaro da kuma kwanciyar hankali mai dorewa.
Dole a fadi gaskiya idan ta kama, suna mukatar gwarin gwiwa da kula mai kyau a yaki da sukeyi da yan ta’adda.
A halin yanzu, Vitalis Kawunda Lee Odikamnoror daga jihar Kaduna, wanda ke ikrarin yana aiki a hukumar sojojin Najeriya ya aiko mana da hotuna, yana korafin rashin abinci mai kyau.
KU KARANTA KUMA: Bode George ya soki APC, Buhari kan tsarin shugabanci
Ya rubuta: “Mutane zancen gaskiya har yanzu bamu ci abinci ba kuma muna yaki da yan Boko Haram.
“Mutanen kirki. Idan mukayi Magana sojoji zasu ce a yanke masa hukunci. Kawai ku sani a kokarinmu yanzu muka gama dafa Indomie. Kalli abunda muke ci ba nama. Kuma mu sojoji ne munayi wa kasarmu yaki. Shiyasa sojoji ke barin aikin. Yunwa zai kashe mu. Gara na bar aikin. Yunwa na sanadin mutuwa. Dan Allah majalisar dinkin duniya ta taimaka mana. Kalli abinci. Sau uku a rana.”
An rahoto cewa sojojin Najeriya dake yaki da yan Boko Haram na kwasan naira dubu arba’in da tara (49k) duk wata a matsayin albashi. Sannan nara dari biyar (500) kudin abinci kullun.
The post Kalli abincin da Sojojin Najeriya ke korafin cewa sun gaji da shi (hotuna) appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.