Tinubu ya bada gargadi mai karfi kamar yadda a karshe ya yi Magana a kan dangantakarsa da Buhari da kuma APC
– Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa ya zama dole a watsar da duk wani hasashe game da fadace-fadace dake jam’iyyar APC a cikin kwandon shara
– Tinubu yace har yanzu yana tsaye don goyon bayan Buhari da jam’iyyar APC
– Jigon na APC ya ci gaba da bayyana cewa shi ba zai bambaro ko wani sabon jam’iyyar siyasa ba
Cif Bola Ahmed Tinubu ya bukaci yan Najeriya da suyi watsi da labaran da ke yawo a gari, game da zargin cewa kawuna ya rarrabu a tsakanin jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa yana tare da Buhari da APC
Wanda ya asassa jam’iyyar ta APC yayi wannan sanarwan ne a cikin wani jawabi gay an Najeriya ta daya daga cikin shafukan APC na Facebook.
A cewar janarwan mai taken: “Ku daina dukkan wadannan shashancin kafofin zumunta, Ina tare da Buhari da APC”.
KU KARANTA KUMA: Sojoji sunyi korafi kan rashin ciyar dasu abinci mai kyau hotuna
Tinubu yace: “Duk karya ne, ina nan lafiya tare da shugaban kasa, ba gudu ba ja da baya, Bana bukatar sai na zauna a fadar shugaban kasa kafin ku san ina gwamnati, mataimakin shugaban kasa Osinbajo na can, Abike Dabiri na nan, Fashola na nan, Lai Mohammed na nan, Fayemi da sauran wasu da dama na nan, ni da shugaban kasa muna tattaunawa lokaci zuwa lokaci kan al’amuran kasa.
A halin yanzu, gwamna Simon Lalong a ranar Litinin 21 ga watan Nuwama ya bayyana cewa gwamnonin APC na kudu da su samu halartan yakin neman zaben APC da akayi Akure, Ohdo a ranar Asabar ba sun aika da ban haukurinsu sun kuma ba da uzuri masu karfi da ya hana su halarta.
The post Tinubu ya bada gargadi mai karfi kamar yadda a karshe ya yi Magana a kan dangantakarsa da Buhari da kuma APC appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.