Shugaban jamíyyar APC ya kwanta dama
Shugaban jamíyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Ogun, Alhaji Roqeeb Adeniji, ya rasu.
APC Logo
Ya rasu ne a yana mai shekarar 79 kuma shekaru 2 kenan bayan rasuwar uwargidansa a wata hadarin mota
A lokacin da muke tattara wannan rahoto, babu cikakken bayanai akan rasuwarsa,amma jaridar Punch ta bada rahoton cewa daya daga cikin yaransa, Bolaji Adeniyi, yace mahaifinsa wanda akafi sani da ‘Baba Computer’ya rasu ne a daren ranan litinin,21 ga watan Nuwamba.
KU KARANTA: Kilaki tayi masa duka kan zai biyata ladan kwanciya da dafaffen Ƙwai
Yace: “ Ya rasu ne bayan an kaishi asibiti a rdaren litinin. Babban mutum ne, babban dan siyasa,kuma mai hankali.”
A watan Oktoban 2014, shugaban jamíyyar ya rasa uwargidansa a wata hadarin motar da ya faru a Akihale Wasinmi na karamar hukumar Ewekoro na jihar.
Gwamnan jihar Ogun, Ibikunle Amosun, ya je taáziyya gidan marigayin bayan hadarin kuma yayi koki da shugaban jam’iyyar.
A biyo mu shafimunmu na Tuwuta: @naijcomhausa
The post Shugaban jamíyyar APC ya kwanta dama appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.