Wani miji ya rabu da matar sa bayan ya ganta alokacin da batada kwalliya
Wata mata a kasar Afirika ta kudu, ta gamu da gamon ta, bayan da mijin ta ya rabu da ita alokacin daya ganta bata da kwalliya, inda ya yanke shawaran rabuwa da ita.
Hoton matan, daga barayin hagu ana iya ganin ta alokacin da batayi kwalliyaba, a inda hoton dake barayin dama kuma ya nuna cewar tayi kwalliya.
Matar yar shekara 35 a garin Mpumalanga a kasar Afirika ta kudu, ta gamu da gamon ta ne bayan da auren ta ya mutu alokacin da sukaje yawon amartaka tsakanin ta da miji nata.
KU KARANTA: Assha: An kama Fasto yayi fyade
An dai bayyana abun ne a jarida, inda aka bayyana cewar, alokacin da mijin ya ga matar nasa a karon farko ba tare da tayi kwalliya ba, saiya tabbatar da cewa matar tashi ta yaudare shi. Sakamakon yanayin yadda yaga fuskan nata ya canza kamar ba itaba. Gadai jaridar.
Jaridar da aka wallafa labarin kenan.
Auren dai daga karshe ya kare ne da saki a tsakanin su, saboda mijin ya kasa gane asalin fuskar daya fada soyayya game da ita. Wani likita mai suna Molapo ya samu takardar bukata daga wajen matar cewar ya taimaka ya gano mata dalilin sakin nata da mijin nata yayi.
Yanzu dai maza sun fara gane yadda mata suke kokarin karama kansu kyau ta hanyar yin kwalliya. Shin kuna ganin wannan shawaran da mutumin nan ya yanke akan matar sa yayi dai dai?
The post Wani miji ya rabu da matar sa bayan ya ganta alokacin da batada kwalliya appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.