Marubuci yace ya kamata Jonathan ya dawo
– Tun bayan saukan Shugaba Goodluck Jonathan, ana ta zai-dawo ko ba zai-dawo ba
– Shekaran Jiya Goodluck Jonathan ya cika shekaru 59 a duniya kuma tsohon Shugaba Jonathan yace ya gama mulki, Dele Momudo yace ai ba ka isa ba
Dele Momodu
Shahararren marubucin nan, Dele Momodu yayi rubutu, inda ra’ayin sa ya sha ban-ban da na tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan. Dele Momodu yace ya kamata Goodluck Jonathan ya dawo, ya tsaya takara zabe mai zuwa.
Dele Momodu yace har yanzu akwai abubuwa a Kasa da suka tabarbare, kuma Shugaba Buhari ya gaza gyara su. Yace hakan ta sa ake kallon Tsohon Shuganan Kasa Goodluck Jonathan da ya dawo.
KU KARANTA: Gwamnonin da za su iya barin APC
BBC ta rahoto cewa mutane suna ta daga hannu suna ihun cewa Jonathan ya dawo, wannan abu ya faru ne lokacin da Goodluck Jonathan ya je ta’aziyar Tsohon Sarkin Musulmi a Garin Sokoto. Dele Momodu yace wasu na ganin farin jinin Shugaba Buhari ya tafi ganin halin da ake fama.
Ana ta rade-radin dai cewa Jonathan din zai dawo, sai dai a shafin sa na kafar Facebook ya rubuta cewa shi fa ya tafi kenan, sai labari. Shugaba Jonathan yace ai yanzu mulki kuma sai ‘ya ‘yan su da jikoki, don su kam sun yi sun gama.
A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa
The post Marubuci yace ya kamata Jonathan ya dawo appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.