Sheriff ya aika ma Makarfi gargadi kan yunkurin shirin canja sabuwar jam’iya
– Ciki ya duri ruwa a yayin da rade- raden da akeyi na bangaren 1 na jam’iyar PDP suke kokarin canja jam’iya, Sheriff yayi tsokaci
– Bangaren Sherif sun tunatar da bangaren Makarfi cewa canja suna ba shine damuwar jam’iyar ba amma akwai wasu matsaloli da suke damun jam’iyar
Bangare 1 na jam’iyar PDP wanda Ali Modu Sherif ke shugaban ta an ruwaito cewa suna taya bangaren Ahmed Makarfi shugaban rikon kwarya na jam’iyar murna na kokarin hada sabuwar jam’iyar da yake kokarin yi.
Akwai rade-raden da ake yi cewa bangaren Makarfi suna kokarin barin jam’iyar PDP su kirkira wata sabuwar jam’iya saboda rikicin da yaki ci yaki cinyewa a jam’iyar ta PDP wanda ya saka rufe ofishin jam’iyar na wata sa watanni.
Makarfi da Sherrif
Walid Jibril shugaban amuntattu na jam’iyar , ya bayyana yunkurin canja jam’iyar a matsayin bala’i ga PDP.
KU KARANTA: INEC ta watsa wa PDP kasa a ido .
Jaridar Daily Trust tayi rohoton cewa Sherif yace ta hanyar mai magana da yawun bakin jam’iyar Bernard Miko cewa yin sabuwar jam’iya ba ze magance matsalar jam’iyar ba.
A wani bayani da muka ji ya kara bayyana cewa sunan jam’iya ba shine matsala ba, rashin adalci da yake faruwa tsakanin shugabanin jam’iyar da magoya bayanta.
Dan haka yan bangaren Sherif suka gargadi Makarfi cewa yan Najeriya ba zasu taba yarda da yunkurin su ba, tunda mutane sun san meye kudurin su.
A yayin da yan bangaren Makarfi suke kokarin canja sheka zuwa yin sabuwar jam’iya, PDP tana masu fatar alheri, amma ana so su tuna cewa ba sunan be matsalar jam’iyar ba, rashin adalcin mutanen da ke ciki jam’iyar.
The post Sheriff ya aika ma Makarfi gargadi kan yunkurin shirin canja sabuwar jam’iya appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.