Boko Haram sun yi barna a Chibok
– Boko Haram sun kai hari a wani kauye kusa da garin Chibok a kudancin jihar Borno
– Kusan ‘yan ta’addan Boko Haram din sun kona kauyen kurmus da kuma sojojin Najeriya sun yi namijin kokari
Rahotanni daga Jaridar The Cables sun bayyana cewa ‘Yan Boko Haram sun kai wani mummunan hari a wani kauye da ke daf da Garin Chibok. ‘Yan Boko Haram din sun kai wannan hari ne wani Gari da bai wuce kilomita 15 ba zuwa Garin Chibok.
Wani mazaunin Kauyen mai suna Hassan Umar, yace an kai wannan hari ne tun karshen wancan makon da ya wuce. Malam Hassan yace ba don Sojojin Najeriya ba, da tuni ‘Yan Boko Haram sun kona kauyen gaba daya.
KU KARANTA: An gano kasuwar Boko Haram
Yan Boko Haram din dai suna kokarin satan abinci ne daga Kauyen, don kuwa mutanen Kauyen sun yi noma wannan karo. Mazauna Yankin dai sun ce Boko Haram din sun addabe su cikin ‘yan kwanakin nan.
An da ice ‘Yan Kungiyar Boko Haram din ba za suyi nisa da Garin Chibok da aka taba sace ‘yan mata kwanaki ba. Kwanan dai ana ta samun hare-hare dabam dabam.
A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa
The post Boko Haram sun yi barna a Chibok appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.