Sojojin Najeriya sun tarwatsa ‘yan Boko Haram
– Sojojin Najeriya sun kashe ‘yan Boko Haram da dama
– Rundunar sojojin Najeriya sun buga da mayakan Boko Haram din ne a hanyar Damboa
– Boko Haram sun kai hari a wani kauye kusa da garin Chibok makon da ya wuce
Sojojin Najeriya sun kashe ‘Yan Kungiyar Boko Haram da dama a wani hari da aka kai jiya, Litinin 9 ga wata. An dai yi nasarar kashe mayakan Boko Haram barkatai, inda wasu kuma su ka sulale, wasu da dama kuwa sun jikkata.
Jaridar Sahara Reporters ta rahoto cewa Rundunar Sojojin Najeriya ta kai wani harin samame ne ga ‘Yan Boko Haram din a Hanyar zuwa Garin Damboa, a cikin Garin Maiduguri na Jihar Borno da wata Runduna guda.
KU KARANTA: An kashe yan Boko Haram
Sai dai Kakakin Rundunar Sojin Kasar bai ce komai ba game da batun. Amma kuma dai wani mazaunin Yankin Chibok ya bayyana cewa Boko Haram sun kawo masu hari cikin makon da ya gabata, yace ba don Sojoji ba, da an tada kauyen.
Kwanan nan kuma aka tabbatar da kisan mayakan Boko Haram guda 11 a Garin Borno. Rundunar Sojojin Kasar Najeriya ce dai ta samu galaba kan ‘Yan kungiyar na Boko Haram a karshen wannan makon.
A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa
The post Sojojin Najeriya sun tarwatsa ‘yan Boko Haram appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.