Sojin Najeriya sunyi nasarar cafke jigogin Boko Haram a wata kasuwa (Karanta)
A safiyar jiya Laraba ne dakarun Operation Lafiya Dole tare da taimakon ‘yan banga suka kama wasu mutane uku a kasuwar shanu dake Maiduguri wadanda ake zargin membobin Boko Haram ne.
Wadanda ake zargin sun hada da Abba Go Dallagio, Abba Fanned da Alhaji Nwariye.
A yayin da ake gudanar da bincike a kansu, sun yi ikrarin cewa sun shigo kasuwar ne ta yankin Mafa da shanu guda 200 domin su sayar.
Sun kuma kara da cewa suna daga cikin masu taimakawa Boko Haram wajen sayar musu da shanu.
A wani labari makamancin haka ma, sojojin sun kama wani jakada kuma dan leken asirin ‘yan Boko Haram mai suna Alhaji Ajid Umar a kasuwar shanun. An gano shanu kimanin 170 ta hannunsa.
Yanzu haka ana kan ci gaba da gudanar da bincike a kansu.
The post Sojin Najeriya sunyi nasarar cafke jigogin Boko Haram a wata kasuwa (Karanta) appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.