Wasu mutane sunyi mutuwar kaskanci a gidan karuwai (Hotuna)
Wasu mutane shida sun rasa ransu a wani gidan karuwai dake garin Umuahia babban birnin jihar Abia.
Wata majiya ta bayyana cewa mutanen dai na kan gudanar da sharholiyar su ne a cikin gidan inda wasun su sun fara jin maye sai haka kurum suka ga an fara ta da hatsaniya, daga bisani bayan rikicin ya lafa, sai aka samu wasu karuwan ‘yan mata su uku da wasu maza kwastomominsu su uku duk sun rasa ransu.
Lamarin da ya fi daurewa jami’an tsaron kai a yayin da suka zo daukar gawarwakin shine yadda mutanen suka mutu ba tare da rikicin ya kai ga an raunata kowa ba.
A wani labarin kuma Rundunar sojin Nigeria ta ce babu wata tutar Boko Haram da aka kafa a kauyuka ukun da ‘yan kungiyar suka kai wa hari a jihar Borno.
Mazauna kauyukan Kubirivour, Boftari and Kuburmbalah da ke kusa da garin Chibok, sun shaida wa majiyar mu cewa mayakan sun yanka mutane takwas, ciki har da wani dagaci.
Hakazalika wata majiyar tsaro da ta fararan hula ta shaida wa majiyar mucewa mayakan Boko Haram sun kafa tutocinsu.
Sai dai mai magana da yawun rundunar sojin Kanar Sani Usman ya ce babu wanda aka kashe, sannan ya musanta rahotannin cewa Boko Haram ta kafa tutarta a kauyukan.
Kanar Usman ya ce mayakan sun kona wasu gidaje kafin sojoji su fatattake su.
The post Wasu mutane sunyi mutuwar kaskanci a gidan karuwai (Hotuna) appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.