Zaben Edo: Gwamna El-Rufai bai je Edo ba
Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya fitar da wata sanarwa da yake karyata zargin da dan takarar PDP na jihar Edo Osagie Ize-Iyamu yayi na cewa wai yaje jihar Edo.
Sanarwar data samu sa hannun mai bashi gwamnan shawara akan kafafen watsa labarai Samuel Aruwan a ranar laraba 28 ga watan Satumba tace wanda Malam Nasir Elr-Rufai bai je jihar Edo ba a ranar laraba, ba kamar yadda wani dan takara ke yayatawa ba. Gwamna Oshiomole ya karyata zancen inda ya tabbatar da cewa Malam Nasir El-Rufai bai je jihar ba. Mun musanta batun nan ne kawai don tabbatar da gaskiyar maganar, amma ya kamata mu sani dokar kasa bata hana kowa zuwa wani sashin kasar nan ba.
Duk da cewa za’a iya hana tafiye tafiye a ranar zabe, hakan baya nufin haramta ma wani zuwa ko ina ba. An taba yi ma Malam Nasir El-Rufai irin wannan zargin yayin zaben gwamnan jihar Anambra, inda aka umarci jami’an tsaro dasu tsare Malam a Otel din daya sauka kawai don ya ja wata jiha a Najeriya don a hana shi yawatawa.
KU KARANTA: Nasiru El-Rufai ya shirya yaki da masu fyade a Jihar Kaduna
Sai dai Malam bai yi kasa a gwiwa ba, ta yadda ya kai karar cin mutuncin da aka yi masa gaban kotu, kuma kotu ta bashi gaskiya.Ya kamata masu neman mulki su bi a hankali wajen cin zarafin dan adam, kuma su kiyaye fadin abin dab a shi ne ba.
Haka ita ma gwamnatin jihar Legas ta bayyana zargin da Ize-Iyamu yayi na cewa wai gwamna Ambode ya shiga garin Edo a ranar Zabe a matsayin kanzon kurege, inda ta tabbatar da cewa gwamna Ambode na kasar waje a yanzu haka.
The post Zaben Edo: Gwamna El-Rufai bai je Edo ba appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.