Ba zai yiwu a dakatad dani ba – Jibrin
Tsohon shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisan wakilan tarayya, Abdul mumuni Jibrin,yayi magana akan dakatad da shi d majalisar wakilai ta yi da zaman majalisa 180.
Abdul mumini jibrin yace dakatad da shi bazata zauna ba
Jibrin ya bayyana hakan ta shafin sada zumuntar sa ta twita jiya laraba ,28 ga watan Satumba, yace shirme kawai suka yi.
Yace : “Babban shirme ne abin nan kuma bazata yiwu ba a ko ina a duniya. Kamar yadda kuka sani, na fada ma lauyana ,Femi Falana SAN ya shigar da kara akan kakakin majalisa Dogara da kuma majalisan tarayya kuma inada tabbacin wannan zance zata je cibiyar lauyoyi kuma za’a yanke hukunci. Inada tabbacin ni zan kasance mai gaskiya”
“Dogara ya zange dantse ya sa an dakatad dani kuma wannan shirme sukayi. Kuma bari in fadi cewa babu wand azan baiwa hakuri a majalisar wakilai. Babu wani dalilin bada hakuri. Ban yi laifin komai ba. Ban taba almundahanan kudi ba.
KU KARANTA:Dan Najeriya yayi nasarar lashe gasar Al-Qur’ani da akayi a kasar Saudiya
Sabanin haka, akwai tuhumce-tuhumcen da na shigar aka n kakakin wanda har yanzu bai amsa ba.”
Dan majalisan ya bayyana babban rashawa da ke faruwa a majalisar bayan an cire shi a matsayin shugaban kwamitin. Za’a hana shi shiga majalisar dokoki domin ladabtar da shi.
Ba zai amshi albashi ba ko alawus. Wasu magoya bayansa sun bayyana hakan a matsayin bangaranci.
The post Ba zai yiwu a dakatad dani ba – Jibrin appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.