APC ta maida Tinubu saniyar ware – Jam’iyyar PDP
– Basarake Bola Tinubu ya bukaci basarake John Oyegun ya sauka daga mukaminsa
– Amma Jam’iyyar PDP a Lagos tace Tinibu bashi da ikon cire shugaban APC
– Jam’iyyar tace Tinibu yayi kokarin maido da martabarsa in yana iyawa
Peoples Democratic Party ta kalubalanci Asiwaju Bola Tinibu daya yi kokarin amsar ikon All Progressive Congress (APC). Akwai rashin jituwa tsakanin Tinibu da shuwagabanni jam’iyyar bayan kiran da yayi ranar Lahadi 25 ga Satumba na basarake John Odigie Ohegun daya sauka daga mukaminsa na shugaban jam’iyyar na kasa dallin yadda aka yi zaben fidda gwani na jihar Ondo.
KU KARANTA: Dan takaran APGA yace anyi magudi a zaben jihar Edo
Daily Trust ta ruwaito Mashood Salvador, shugaban PDP na Lagos na cewa zai yi wuya Tinibu ya cire Oyegun. Yace, zai yi wuya Tinibu ya amshi ikon jam’iyyar domin kamar an sallameshi daga jam’iyyar a wayanceq. Salvador, yace yanzu ne Tinibu zai iya nuna shi jigo ne a siyasance in ya amshe ikon jam’iyyar.
The post APC ta maida Tinubu saniyar ware – Jam’iyyar PDP appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.