Jami’an tsaro sun kulle ofishin Abdulmumini Jibrin
Jami’an tsaro sun kulle ofishin tsohon shugaban kwamitin kasafin kudi a majalisar wakilan tarayya, Abdulmumini Jibrin.
dan sanda na kokariin kulle ofishin
Jami’an tsaro sun kulle ne bayan dakatad da shi da akayi sanadiyar kin gurfanar da kansa gaban kwamitin ladabtarwa tattare da tuhumar aragizon kasafin kudin da ya yayi ma shugabannin majalisar.
KU KARANTA: Ba zai yiwu a dakatad dani ba – Jibrin
A ranan laraba, 28 ga watan Satumba majalisar wakilan tarayya ta dakatad da Jibrin na tsawon zaman majalisa 180. Kana kuma ba zai iya rike wata mukami a wannan majalisar ba har karewan wa’adin ta.
Shi kuma Abdulmumin Jibrin ya bayyana cewa wannan abu da sukayi shirme ne kuma ba zai yiwu ba.
The post Jami’an tsaro sun kulle ofishin Abdulmumini Jibrin appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.