Zaben Jihar Edo: Yan Najeriya sun tofa albarkacin bakinsu
Dan takarar jam’iyyar APC, Godwin Obaseki ne ya lashe zaben takaran gwamnan jihar Edo.
Zaben da ya gudana a ranan laraba, 28 ga watan Satumba, inda mutane suka fiti kwansu da kwarkwatan su domin kada kuri’arsu.
Hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta INEC ta sanar da sakamakon zaben a yau Alhamis inda zakaran ya samu kuri’u 319,483 kuma abokin adawarsa Fasto Ize iyamu ya samu kuri’u 253,173.
Yan Najeriya sun mika sakon taya murnansu ga ga Obaseki yayinda wasu kuma suke tada jijiyoyin wuya akan rashin amincewarsu da sakamakon zaben.
KU KARANTA: APC ta maida Tinubu saniyar ware – Jam’iyyar PDP
Ga maganganun yan Najeriya
“PDP, cin zabe ya wuce canza sunan shafin sada zumuntar twita.
“Muna taya Obaseki murna a matsayin gwamnan jihar Edo mai jiran gado. Masu tada jijiyoyin wuya su je kotu.
“Jama’an jihar Edo sun yi magana da yawu daya, suna son cigaba kuma sun samu, Muna taya Obaseki murna, muna taya APC murna.”
The post Zaben Jihar Edo: Yan Najeriya sun tofa albarkacin bakinsu appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.