Zaben Edo: Obaseki yayi wa Ize-Iyamu fintinkau
– Dan takarar Jam’iyyar APC a zaben jihar Edo, Godwin Obaseki na gaba wajen kuri’un da aka kirga zuwa yanzu
– Godwin Obaseki ya lashe zaben kananan hukumomin Igueben da Uhunmode na Jihar
– Yanzu haka dai hukumar zabe ta kasa, INEC na ta kokarin fitar da sakamakon zaben
Sakamakon zaben da suke fitowa daga bakin Hukumar zabe ta Kasa mai zaman-kan ta watau INEC sun nuna cewa dan takarar APC, Godwin Obaseki ne ke kan gaba, har yanzu a zaben. Sakamakon zaben da ya fito daga bakin ita kan ta Hukumar zabe ta Kasa, INEC sun tabbatar da cewa Godwin Obaseki ya samu nasara a Karamar Hukumar Igueben da kuma ta Uhunmode.
Dan takarar APC, Godwin Obaseki ya lashe kuri’a 7802 a Karamar Hukumar Igueben yayin da Fasto Ize-Iyeamu ya tashi da 7560. A karamar Hukumar Uhunmode kuwa, Obaseki ya samu kuri’a 10911, inda shi kuma Ize-Iyeamu na PDP ya tashi da 8667. Kawo yanzu haka dai, dan takarar APC, Obaseki ya tserewa abokin adawar san a PDP, Andrew Ize-Iyeamu.
KU KARANTA: Zaben Gwamna a Jihar Edo
INEC ta tabbatar da cewa Godwin Obaseki na APC ya lashe sakamakon Kananan hukumomi har biyar, inda shi kuma dan takarar PDP yake da daya, karamar Hukumar Esan ta Arewa. Dan takara Obasakei na APC yana da kuri’a 66882, shi kuma dan takarar PDP yana da 62093; tazarar kusan 6000.
Sakamakon baya dai kamar yadda Jaridar Daily Trust ta rahoto, sun nuna cewa Obaseki ya samu nasara a Kananan Hukumomin Owan West, da Egor. Mutane kusan Miliyan biyu ne dai ake sa ran za su kada kuri’ar ta su wajen zaben sabon Gwamnan Jihar Edo. Shekaran nan ne wa’adin Adams Oshiomole ya cika.
The post Zaben Edo: Obaseki yayi wa Ize-Iyamu fintinkau appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.