Samun Biafra ba abu ne mai yiwuwa ba – Okechukwu
– Osifa Okeckukwu ya shawarci Igbos su shirya amsar shugabancin kasar a 2023
– Babban daraktan VON yace an wuto yiwuwar samun Biafra tun 2014, inda yace halin siyasar da ake ciki zai hana yiwuwar samun Biafra
Osita Okechukwu
Osifa Okechukwu yace yiwuwar samun Biafra ya sha kashi a shekarar 2014 wajen taron kasa wanda akayi lokacin mulkin Goodluck Jonathan. Kasar na fuskantar kiraye-kifayen ‘yancin Biafra, na baya bayannan shine boren kowa ya tsaya gida wanda aka yi a kudu maso gabas ranar Juma’a 23 ga Satumba.
KU KARANTA:Siyasa da tattalin arzikin Arewacin Najeriya bayan yanci kai a 1960
Vanguard ta ruwaito Okechukwu wanda shine babban daraktan muryar Nageriya koko Voice of Nigeria na fadin haka yayin da yake magana da kungiyar Ohaneze Ndigbo bangaren Abuja, inda yace rashin hadin kai ya jaza suka kasa magana da baki daya wajen taron kasa lokacin mulkin Jonathan.
Yace: ” Shawarar da aka zartas na kin koma ma tsarin bangarori a taron kasa na karshe da kuma rashin hadin kan Igbo kan tsarin, shi zai sa neman Biafra yaki yiwuwa.”
The post Samun Biafra ba abu ne mai yiwuwa ba – Okechukwu appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.