An harbe yan fashi biyu har lahira a yayinda suke fashi a jihar Lagas
-Yan sandan jihar Lagas sun harbe yan fashi biyu har lahira
-An kashe yan fashin ne bayan wani arangama na musayar wuta da ya afku a tsakanin yan fashin da yan sanda a jihar
-Kwamishinan yan sanadan jihar Lagas, Fatai Owoseni, ya tabbatar da kisan
Jami’an Yan sandan jihar Lagas sun harbe wasu yan fashi da ba’a san sunayensu ba tukuna har lahira a unguwar FESTAC na jihar Lagas.
Kwamishinan yan sandan jihar Lagas Fatai Owoseni
Jaridar Punch ta ruwaito cewa an sanar da Yan sandan yankin FESTAC game da yan fashin wadanda suka kori matayen dake unguwar, wanda suka fito daga banki a mararabar Apple.
An bayyana cewa kungiyar mutane hudu suna ta musayar wuta da jami’an yan sanda lokacin da lamari ya afku, wanda ya faru da misalign karfe 12 na ranar juma’a, 26 ga watan Augusta. An bayyana cewa biyu daga cikin yan fashin sun tsere yayinda yan sanda suka harbe sauran biyun har lahira sum kuma kai gawansu gurin ajiyar gawa.
KU KARANTA KUMA: Jami’in INEC ya dawo da miliyan 20 na cin hancin zabe
A cewar yan sanda, yan fashin su hudu ne, sun zo a kan Babura guda uku. Suna ta lura da mutanen dake barin harabar bankin, musamman mutanen dake rataye da jakar hannu. Idan suka mace rataye da jaka, wani dan leken asirinsu dake kusa da machine din kudi (ATM) sai yayi ma sauran alama su kuma sai subi sahun wanda aka nuna masu zuwa wani guri, sai suyi mata sata. Suna dauke da bindiga kuma suna iya harbawa idan suka ga dama.
Kwamishinan yan sanda na jihar Lagas, Fatai Owoseni ya tabbatar da kisan. Yace jami’an sun kuma kama wasu masu fashi a kan babur a yankunan Lekki, Ajah da kuma Egbeda na jihar
The post An harbe yan fashi biyu har lahira a yayinda suke fashi a jihar Lagas appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.