Bam ya fashe dab da fadar shugaban kasa
Wata mota dauke da bama-bamai ta tarwatse a wajen wani otal da ke Mogadishu, babban birnin Somalia.
Har wa yau, otal din yana dab kofar shiga fadar shugaban kasa. Akalla mutane biyar ne suka mutu kuma wani wanda ya shaida yadda al’amarin ya faru ya fada wa majiyar mu cewa mutane da dama sun jikkata.
Tuni kungiyar al-Shabab mai alaka da al-Qaeda ta dauki alhakin kai harin. Otal din mai suna Somali Youth League ya kasance sanannen wurin haduwar jami’an gwamnati kuma wannan ba shi ne karon afrko ba da aka kai masa hari.
The post Bam ya fashe dab da fadar shugaban kasa appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.