Arsenal ta siyo Perez daga Deportivo
Arsenal ta dauki Lucas Perez daga Deportivo La Coruna kan kudi fan miliyan 17.1.
Arsenal
Dan kwallon tawagar Spaniya, wanda bai fara buga mata tamaula ba, ya ci wa Deportivo kwallaye 17 a wasanni 37 da ya yi, tun lokacin da ya koma Spaniya daga PAOK ta Girka. Arsenal na dab da sanar da daukar dan wasan Valencia, Shkodran Mustafi kan kudi fan miliyan 35.
Tun farko Arsene Wenger ya sayi ‘yan wasan tsakiya Granit Xhaka da Kelechi Nwakali da mai tsaron baya Rob Holding da mai cin kwallaye Takuma Asano a bana.
The post Arsenal ta siyo Perez daga Deportivo appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.