Shin Kocin Italy Ze Maye Gurbin Antonio Conte A Chelsea.
-Giampiero Ventura cikin raha yace ze maye gurbin Antonio Conte a Chelsea.
-Ventura ya maye gurbin Conte a Bari da Italy.
-Mai horarwar Italy yace tsohon kocin Juventus yana da sa’a.
Giampora Ventura yayi raha cewa kila ze maye gurbin Antonio Conte a kungiyar Chelsea lokacin da ze dena aiki da kasar Italy. Ventura ya ambaci Conte a matsayin mai sa’a, ya maye gurbin Conte a matsayin mai horarar Bari da na kasar Italy.
Giampiero Ventura
Sabon kocin Italy Giampiero Ventura ya bar kungiyar Torino dan ya horarar da kungiyar kwallon kafa ta kasar Italy. Ventura ya amshi aikin horarwa na Italy bayan Conte ya bar aiki da Italy inda ya tafi kungiyar Chelsea bayan kocin yakai kasar ta Italy wasar ta 2 karshe a euro 2016.
Bayan Conte ya taimaka ma kungiyar ta Bari zuwa gasar serie B a shekara ta 2008-09, an nada Ventura ya maye gurbinsa. Dan shekara 68 ze iya maye gurbin kwararren mai horarwar.
Antonio Conte
“Na rike kungiyar Bari bayan yaci gasar seria B, kuma kowa a kungiyar yana kaunar shi”Ventura ya fada ma mane ma labarai. “Conte yana da sa’a a gani na, saboda lokacin da nake kungiyar Bari munyi nasara kuma munyi abubuwa masu amfani.
Nazo kungiyar kwallon kafa ta kasar Italy bayan kayatattar Euro 2016 da Conte yaje da kasar ta Italy. Zan gani in zan iya cigaba daga inda ya tsaya.Ina tunanin zan horar da Chelsea in ya bar Chelsea , shi yasa ina shirye da fada da turancina.
Antonio Conte ya cima kungiyar Chelsea wasar premier league 3. “Nayi magana da Conte mintuna 3 da suka wuce,na tambaye shi ya yake? Yace yana lafiya, turancinshi yana da kyau.
Ventura ze fara wasa a matsayin mai horarwar kasar Italy da kasar faransa a wasar sada zumunci ranar alhamis, kafin doka wasar share fagen zuwa world cup da kasar Israel kwana 4 bayan wasar sada zumunci.
The post Shin Kocin Italy Ze Maye Gurbin Antonio Conte A Chelsea. appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.