Tandadin da EFCC ta yiwa Dogara da sauran jami’an majalisa
-Hukumar EFCC za ta binciki Kakakin Majalisar Wakilai bisa zargin aringizo a kasafin kudi
-Wasu kungiyoyi masu zaman kansu sun yi zanga-zangazuwa ofishin EFCC kan batun kasafi kudin
-Hukumar ta ce ba sani ba sabo
Kungiyoyin a yayin gudanar da zanga-zangarsu a ofshin EFCC
Hukumar hana yiwa tattalin arziki zagon kasa EFCC, ta yi alkawarin gurfanar da duk wadanda suke da hannu a zargin aringizo a kasafin kudi a Majalisar Wakilai ta Kasar.
Wannan tabbaci ya fito ne daga bakin wani babban jami’i a hukumar, Iliyasu Kwarbai a lokacin da wasu kungiyoyi masu zaman kansu suka yi wata zanga-zangar lumana a ofishin hukumar da ke shiyyar Lagos a ranar 29 ga watan Agusta.
KU KARANTA: EFCC ta kai ga Olu Falae kan N100 miliyan na makamai
A cewar jaridar Vanguard, Mista Kwarbai ya ce, hukumar ta karbi takardun koke da yawa kan batun daga jam’ar kasa, kuma tuni hukumarsa ta soma bincike kan lamarin a Abuja, sannan ya kuma ce, “Ba sani ba sabo a aikin EFCC, duk wanda muka kama da hannu a cin hanci da rashawa komai girmansa komai kakantarsa ba za mu sauarara masa ba…..,”
KU KARANTA: Dakunan manyan bakin EFCC a Abuja (Hotuna)
Kungiyoyin sun gudanar da zanga-zangar ne zuwa ofishin hukumar suna nuna mamaki gami da takaicin cewa, shugabannin majalisar da ake zargi watau Kakakin Majalisar Wakilai, da Mataimakinsa, da Shugaban masu rinjaye, da shugaban marasa rinjaye, ana zarginsu da hannu a cikin wannan badakalar, amma ba a gayyace su don amsa wasu tambayoyi ba, ba a tuhumesu ba, ba a kuma dauki wani mataki na hukunta su ba.
The post Tandadin da EFCC ta yiwa Dogara da sauran jami’an majalisa appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.