Wenger na fuskantar caccaka daga ‘yan Arsenal game da yiwuwar tashin Wilshere
A shirye Arsenal yake da ya bayar da aron dan wasan kulob din na tsakiya, Jack Wilshere da wani babban kulob.
Arsene Wenger
Dan wasan, shekara 24 wanda yake yawan samun rauni, ya buga leda sau uku ne kawai ga Arsenal, a kakar wasannin da ta gabata sakamakon raunin da ya samu a kwaurinsa. Wilshere dai ya buga wa Ingila wasanni guda shida a lokacin bazara, duka suka hada da wasanni uku a gasar Euro 2016.
Sai dai kuma sunan Wilshere bai fito ba a jerin sunayen ‘yan wasan da Sam Allardyce ya fitar a wannan makon. Kulob din Arsenal dai ya sayi dan wasan tsakiya, dan kasar Switzerland,Granit Xhaka a kan £35m.
The post Wenger na fuskantar caccaka daga ‘yan Arsenal game da yiwuwar tashin Wilshere appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.