Yan baranda sun kashe kwamandan CJTF a jihar Kaduna
–An kashe kwamandan CJTF, Buhari Ahmad Tanko
–An bada rahoton cewa wasu yan bindiga ne suka kashe shi a jihar Kaduna.
–An kashe kwamandan ne yayinda ya ke yunkurin taka ma wasu yan ta’adda birki
An kashe kwamandan CJTF,shiyar Kakuri, karamar Hukumar Kaduna ta kudu mai Buhari Ahmad Tanko a jihar Kaduna. Jaridar the Nation ta bada rahoton cewa wasu yan baranda ne suka kashe shi .
Kakakin jami’an yan sandan jihar Kaduna, ASP Aliyu Usman ya tabbatar da faruwan. Ya ce , an kasha marigayi tanko yayinda yake kokarin hana wasu yan baranda fasa kamfanin masaka ta jihar Kaduna watau Kaduna Textile Limited domin yin sata.
ASP Usman yace abin ya faru ne misalin karfe 3:26 na dare a ranar litinin,29 ga watan agusta. Shi yasa jami’an yan sanda basi kama koma dake da alaka da kisan ba. Yace amma ana kan gudanar da bincike akan al’amarin kuma sai an gurfanar da su a gaban hukuma.
Anyi yunkurin ganawa da iyalin marigayin amma ba’a same su ba a lokacin rubuta wannan labari. Amma wani mamban CJTF a kakurin wanda aka sakaye sunansa ya sha alwashin cewa wanna kisa ba zai hanasu cigaba da tabbatar da tsaro ga mutanen anguwa ba,suna kira ga gwamnati jihar da ta karfafa su a maimakon yunkurin dakatar da su kamar yadda muke ji kafafan yada labarai.
KU KARANTA : An kashe wani shararren lauya a Jihar Ribas
“Mun fi kowa sanin unguwar saboda mune mazauna wurin. Gwamnati zata iya kara horar da mu saboda cigaba da gudanar da aikin mu. Abinda ya faru ba zai hana mu yin fatrol a unguwa ba musamman da daddare . kuma sai mun gurfanar da wadanda suka kashe Buhari.” Yace.
The post Yan baranda sun kashe kwamandan CJTF a jihar Kaduna appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.