Dalilin da yasa yan sanda suka kai mutumin da ya sanya wa karensa Buhari kotu
-Yan sandan Najeriya sunce an kama Joe Chinakwe, mutumin da ya sanya wa karensa suna Buhari saboda yayi yunkurin haddasa rashin zaman lafiya a tsakanin jama’a
-Yan sandan sun bayyana ra’ayin mutane kan danganta shugaban kasa Muhammadu Buhari da hukunta mutumin a matsayin rashin adalci
-Yan sanda sunce abunda Chinakwe yayi yaso ya haddasa rikicin kabila a Ketere, Sango Ota, a karamar hukumar Ado Odo Ota na jihar Ogun
Hukumar yan sandan Najeriya sun bayyana dalilin da yaka suka mika Joe Chinakwe, mutumin da ya sanya ma karensa suna Buhari a gaban kotu.
A cewar mataimakin sufeto janar nay an sanda,na Zone II, Abdulmajid Ali, wadda yayi maka ta wani sanarwa da za hannun kakakin yan sandan yankin, Muyiwa Adejobi, yace an kama Chinakwe an kuma tsare shi saboda yunkurin tada rashin zaman lafiya a cikin jama’a.
KU KARANTA KUMA: Gwamnatin tarayya ta karbi shari’ar cin hanci da rashawa daga hannun EFCC, da ICPC
Yan sanda sun bayyana furucin da ake na danganta hukunta mutumin da shugaban kasa Muhammadu Buhari a mastayin rashin adalci.
Yan sanda sun ce abunda Chinakwe yayi zai iya haddasa rikicin kabila a Ketere, Sango Ota a karamar hukumar Ado Odo Ota na jihar Ogun, in badan yan sanda sun shiga lamarin a kan lokaci ba.
The post Dalilin da yasa yan sanda suka kai mutumin da ya sanya wa karensa Buhari kotu appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.