Femi Adesina ya gana da Turaki Hassan a fadar shugaban kasa
Ta tabbata ashe shugaban kasa ya kan wakilta hadimansa su gana da jama’a a madadinsa, musamman ma Femi Adesina, mai bashi shawara kan kafafen watsa labarai.
Femi Adesina tare da Turaki Hassan
A ranar litinin 29 ga watan agusta ne ne Mista Femi Adesina ya karbi bakoncin Turaki Hassan, mai magana da yawun kaakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara, tare da wasu gagga gaggan yan siyasa a fadar shugaban kasa dake Abuja.
Ga kadan daga cikin hotunan ganawar nasu.
Zuwa yanzu dai shugaban kasa ya dawo daga tattakin da yayi zuwa kasar Kenya, bayan halarci taron da kasar Tokyo ta shirya don cigaban kasashen Afirka karo na shidda daya wakana a kasar Kenya.
The post Femi Adesina ya gana da Turaki Hassan a fadar shugaban kasa appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.