Rundunar Sojin Najeriya sun kashe barayin dabbobi 20
–Rundunar Sojin Najeriya sun kashe barayin awakai 20 a wata farmaki da ta kai a jihar Zamfara.
–Sojin sun kwato bindigan AK 47 10 a harin.
Akalla dakarun sojin najeriya sun kashe barayin shanaye 20 a wata hari da ta kai a jihar zamfara.
Kwamandan 223 Light Tank Battalion, Lt-Col Aliyu Adamu wanda ya bayyana hakan yace Hakazalika sun rusa gidajensu dake Dajin Dansadau. Yace sojin sun kwato bindigan AK 47 10 a harin.
“Mun samu nasara a yakin mu da barayin shanaye, kana mun kashe 20 saga cikinsu. Mun kuma samu daman kwato bindigan AK 47 10 a harin. Sauran kauyukan da aka kai harin sun kunshi Malele, Yarwutsiya, Babar doka, Ruwan Tofa da sauran su.”
Zaku tuna cewa Sarkin Ilori, Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari,ya tsarkake Fulani Makiyaya daga laifuffukan da ake jingina musu na kai hare-hare a fadin kasa.
Sarkin yace makiyaya masu zaman lafiya ne, kuma da kyakkyawan alaka na zamantakewa da bare. Yana kira ga yan najeriya da su cigaba da zaman lafiya domin samun hadin kai. Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari yace hare-haren ake kaiwa a fadin kasa da sunan Fulani makiyaya .
KU KARANTA : Sojoji sun kama masu garkuwa da mutane
A bangare guda,gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose ,ya sanya hannu a cikin sabuwar doka na haramta wa Fulani makiyaya a yankin kudu maso yamma. Ya sanya hannu ne a ranan litinin, 29 ga watan agusta a gaban sarakunan gargajiya kimanin 3.
The post Rundunar Sojin Najeriya sun kashe barayin dabbobi 20 appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.