Nayi ma Wenger magiya ya kawo ni Arsenal kyauta – Rio Ferdinand
Shahararren tsohon dan wasan kungiyar Manchester United Rio Ferdinand ya bayyana cewa ya taba rokan mai horar da kungiyar Arsenal Arsene Wenger da zummar ya kawo shi kungiyar a kyauta a shekarar 2014.
Kwantaragin Ferdinand wanda a yanzu mai tattauna harkar kwallo ne ya kare a shekarar 2014, inda ya sadaukar da kansa ga kungiyoyi da dama. Ferdinand ya koma zuwa kungiyar QPR ne kafin yayi murabus daga harkar kwallo gaba daya, ind ya buga musu wasanni 11 kacal.
A yan kwankin nan ne Ferdinand ya bayyana cewa ya taba rokar Arsen Wenger ya kawo shi Arsenal, duk da irin adawar dake tsakanin kungiyar da Manchester United. Wannan batu ya fito ne a lokacin da wani ke bashi shawarar a shafin twitter kan ya buga ma Arsenal wasa, inda shi kuma ya kada baki yace “ai na taba rokan Wenger”
The post Nayi ma Wenger magiya ya kawo ni Arsenal kyauta – Rio Ferdinand appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.