Tattalin arzikin kasa: Okorocha na bukatar daukar matakan gaggawa
-Okorocha yayi amanna cewa dole ne shugaban kasa ya dauki matakan da ya kamata kan rugujewar tattalin arzikin kasa
-Gwamnan Imo ya ce ya amince idan ‘yan Najeriya suka bada hadin kai za’a iya shawo kan matsalolin tattalin arzikin kasar
-Okorocha ya karyata rohotanni dake cewa ya je waje neman magani, yace ya je Amurka ganin jikansa
Yayin da gwamnatin tarayya ke kokarin shawo kan ‘yan Najeriya cewa ba matsala game da tattalin arzikin kasar, gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha ya baiwa fadar shugaban kasa mamaki da kiransa na a dauki matakan gaggawa game da tattalin arzikin kasar yayin da yake magana da jaridar Leadership, inda yace:
” Ba laifi, kuma bisa ga gaskiya ya kamata mu dauki matakan gaggawa kan tattalin arzikin Najeriya yanzu- yanzu, kuma ana bukatar goyon bayan kowa da kowa domin farfado da tattalin arziki. Garemu da kuma ‘yan Najeriya masu bulaguro waje, ya kamata mu kauda son zuciya mu fuskanci abinda ke gabanmu “ yayin da Okorocha ke amsa tambayar da aka yi masa kan abinda zai ce game da bukatar shugaba Buhari na neman ikon gaggawa daga majalisar kasa.
KU KARANTA : Wurare guda 6 da ake neman mai a Najeriya
A wani bangaren kuma, ‘yan Najeriya na amfani da shafin sada zumunta na Facebook suna nuna zakuwarsu da su ga canjin da aka yi masu alkawari, suna masu kira ga tsohuwar ministan kudi Ngozi Okonjo-Iweala da ta taimaka wajen farfado da tattalin arzikin kasar, domin ga alama abin ya sha karfin gwamnatin kasar. A cikin shekara guda da ta wuce, gwamnatin Buhari ta zargi Okonjo-Iweala da cin hanci da rashawa domin bata mata suna a matsayinta na wata jigo cikin harkokin kudi da kuma wata wadda tayi fice a duniya
The post Tattalin arzikin kasa: Okorocha na bukatar daukar matakan gaggawa appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.