Wani direba ya murkushe ma’aikacin tafiye-tafiyn jihar Legas
A ranan litinin , 15 ga watan Augusta, an bada rahoton cewa wani direba mai suna Sunday Agbariko ya murkushe kafan wani ma’aikacin rage cinkoso a titinan jihar legas mai suna ,Olayemu Isiaka.
Sunday ya murkushe ma’aikacin ne a ofishin LASTMA ne da ke ojota yayinda ake biyoshi a guje domin laifin tukin ganganci. Bayan an kwace mukullin motar Sunday, ya nemi daya daga cikin ma’aikatan ya bashin mukullin domun daukan wani abu a cikin mota.
KU KARANTA : Mutane 5 sun mutu, 13 sun jikkata a hatsarin gadar Legas
Jaridar Punch ta bada rahoton cewa yayinda ya amsa mukullin ya shiga motarsa, kawai sai ya tayar da ita . a yunkurin arcewa, ya murkushe kafan ma’aikacin da ke zaune a bakin kofa . an kai ma’aikacin asibiti da gaggawa a asibitin da ke Igbobi.
Ya kira ruwaba lema.
The post Wani direba ya murkushe ma’aikacin tafiye-tafiyn jihar Legas appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.