Wata kabila a kasar indonisiya masu kona Gawawwakin su
–Akwai wata kauye a kasar Indonisiya masu gasa gawawwakin su a maimakon birne su.
–Sunan kauyen Wogi kuma garin yan kabilan Dani ne a New Guinea.
– Babu hanyar motan da zai kai mutum kauyen sai da ta jirgi mai saukar angulu.
Tribe chief, Eli Mabel posing for photographers with his mummified ancestor, Agat Mamete Mabel, outside a typical home. Photo: Daily Star UK. An gano wata kauye a kasar indonisiya inda basu birne matattun su , sun gasa su a wuta kuma su ajiye su.
Jaridar Daily star UK ta bada rahoton cewa yan kabilan Dani da ke kasar Indonisiya sun kasance suna ajiye gawawwakin su baya sun kona su. Duk da cewan an samu rahoton cewa sun daina yanzu, yan kabilan Wogi ,mazauna kauyen kusa da birnin kasar ,Wamena,suna rike wasu gawawwaki har yanzu.
Game da cewar yan kauuen, kona gawa da kuma yi masa hayaki makonni bayan rasuwar shi,nuni ne ga irin girmamawan da ake ma wanda yam utu al’adun Dani.
KU KARANTA : Jarirai 12 sun mutu sanadiyar gobara cikin asibiti
A kwanakin nan, irin wannan dabi’a na mutanen ya jawo hankalin mutane zuwa garesu ,kimanin mil2,000 daga babban birnin kasar Jakarta. Jaridar Daily Star UK ta bada rahoton cewa baki na ba idanuwansu abinci a bikin zagayowar Baliem da ake yi .
Lokaci na farkon da yan kabilan Dani suka tarbi baki shine a shekarar 1909.wani bangarensu ma ba’a san dan dasu ba sai lokacin da wata jirgin saman amurka ta gano su a shekarar 1938.
The post Wata kabila a kasar indonisiya masu kona Gawawwakin su appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.