Abubuwa 5 da aka sani akan Ahmad Salkida
Bisa ga sabuwar bidiyon da yan kungiyar boko haram suka saki,wanda ke nuna yan matan chibok dinga aka kama, hukumar sojin najeriy sun ce suna neman wasu mutane 3 ruwa a jallo. Diraktan hulda da mutanen hukumar soja, kanal sani usman kukasheka ne ya bayyana haka.
“Ko shakka babu wadannan mutanen nada masaniya game da boko haram kuma suna ganawa da su. Don haka dole ne su zo su fada mana inda suke ajiye yan matan da kuma wasu mutanen da suke garkuwa da shi.” Yace.
Domin haka muna kira da duka yan najeriya da masu bukatan zaman lafiya da su bamu masaniya game da inda suke. Wadanda ake nema ruwa a jallo sune Ahmad Salkida, (Ambassador) Ahmed U. Bolori and Aisha Wakil.
Shin menene muka sani game da Ahmad Sakilda
- Ahmad Sakilda dan jarida ne wanda ke da shafin yanar gizon sa kuma yana rubua ga jaridar Premiuim Times.
- Ahmad Sakilda dan asalin garin biu ne,jihar barno. La’alla wannan ne abinda ya bashin ikon ganawa da mayakan boko haram. Shine dan jaridan karshe da daya yi hira da wanda ya kirkiri boko haram ,Muhammad yusuf a shekara 2009, gab da a kashe shi.
- Ba mazauni Najeriya bane, ya koma kasar dubai ne bayan an fara tuhumarsa da cewan shi dan boko haram ne. shine mai sulhu tsakanin boko haram da hukumar Sojin Najeriya.
- A ranar talata,29 ga watan yuli, jami’an yan sandan najeriya sun kama shi kuma ya ce an bada umurnin su kashe shi . amma daga baya suka fasa.
- Akwai lokacin da ya kwashe kwanaki 5 a tsare tare da wasu mambobin boko haram a hedkwatan yan sanda da ke Maiduguri. Wannan shine lokacin da aka kashe shugaban kungiyar ,Muhammad Yusuf.
- ya bayyana cewan ya shirya mika kansa kuma yana hanyar dawowansa Najeriya.
The post Abubuwa 5 da aka sani akan Ahmad Salkida appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.