Almajirai sun sha da kyar a jihar Lagas
An gurfanar da wani mutumi da yar’sa a gaban wani Kotu kan zargin cewa sunyi kokarin kashe wasu Almajirai wanda suka dauka taimakon su zasuyi.
Abunda ya kamata yaza lokacin bayarwa da godiya, ya juye ya zama lokacin ‘Allah gode maka ina raye’ yayinda aka ceto wasu almajirai daga abunda babu tantanma da ya zama ajalinsu a aranar 5 ga watan Augusta.
Bisa ga rahotanni, wasu almajirai a kusa da unguwar Offin a yankin Balogun na birnin jihar Lagas, sun karbi abunda suka dauka jin kai ne, lokacin da Salamat Yusuf mai shekaru 18 ta basu sadakan kosai. A yayinda suka bude kosan domin su ci, daya daga cikin mabaratan ya hangi allura a cikin kosan da yake kokarin ci.
Lokacin da yaje ya sami Salamatu da batun abinda ya gani, Tace babanta Mohammed Yusuf ne ya bata kosan, ya kuma umarce ta da ta raba masu sadaka.
A lokacin da aka gurfanar dasu kaban babban Kotun Tinubu, mahaifin yarinyar da ita kanta yarinyar sun karyata cajin da akeyi a kansu na cewa sunyi yunkurin aikata kisan kai.
Kotu
KU KARANTA KUMA: Kai ba soja bane a yanzu- Sarkin Lagas ya fada ma Buhari
Ga abunda mai shari’an barista Ben Ekundayo yace:
“Mohammed da Salamatu sun aikata abun da niyar cutar da rayyukan mabarata. Malamin musuluncin ya aika yar sa ta ba mabaratan kusa da massalaci sadakan kosai, amma a lokacin da daya daga cikinsu (almajiran) ya bude kosan, ya tsinci allurai a tsakiyan kosan. Sai ya sanar da suran mabaratan; daya daga cikinsu, wanda ya san yarinyar da kuma makarantar da take koyarwa, ya jagorance su, aka kuma cafke ta.”
An bayar da belin wadanda ake zargin a kan naira 500,000, yayinda aka daga karan zuwa ranar 29 ga watan Satumba.
The post Almajirai sun sha da kyar a jihar Lagas appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.