Damar karshe ga Arsenal wajen sayen dan wasa
Kamar dai yadda jaridar Daily Mirror ta ruwaito, kungiyar Valencia tana bukatar £25m daga wajen Arsenal kafin ta saki dan wasan bayan ta Mustafi. Kudin da ita kuma kungiyar ta Arsenal take jan kafa wajen bayarwa.
A baya dai mun ruwaito cewar mai horarda yan wasan Arsenal din Arsene Wenger ya bayyana kudirin sa wajen ganin ya siyo yan wasan baya da zasu kara ma kungiyar tasa karfi inda ya bayyana sha’awarsa ga dan wasan na kungiyar Valencia Mustafi.
Wakilin dan wasan dai Ali Bulut yace: “e tabbas dan wasa na da kuma kungiyar ta Arsenal sun cimma matsaya tuni, yanzu dai kawai ana jiran kungiyoyin biyu su cimma yarjejeniyar tasu a tsakanin su.”
Bulut ya cigaba da cewa: “ya zuwa yanzu abunda kawai zan iya cewa kenan game da dan wasan nawa. Sauran bayanin kuma yana a tsakanin kungiyoyin biyu watau Arsenal da kuma Valencia.”
Mai karatu zai iya tuna cewar yan wasan bayan Arsenal a halin yanzu suna jinya ne wadda kuma ka iya tsaida su daga wasa har nan da tsawon watanni da dama. Yan wasan dai sune Per Mertesacker, Gabriel da kuma Koscielny.
The post Damar karshe ga Arsenal wajen sayen dan wasa appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.