Kaicho! An kama Alhajin Nigeria da goro a Saudia
-An kama wani alhaji daga Najeriya da goro
-Ma rikon mukamin jakadan Najeriya ya tabbatar da labarin
-Gwamnatin Saudiya ta tanadi tsattsauran hukunci
Jami’an kasa mai tsarki sun kame wani Alhaji daga Najeriya da Goro wanda hukumar ta haramta.
Wasu mahajjata a yayin da suke shirin tafiya kasa mai tsarki
Rahotannin na cewa alhajin wanda har yanzu ba a bayyana ko wanene ba, da kuma jihar da ya fito, an kama shi ne da ‘yan kwayoyin goron guda 10 a ranar Litinin 15 ga watan Agusta.
Kafar yada labarai ta PM News wacce ta bayar da labarin, ta ce mai riko da mukamin jakadan Najeriya a kasar Saudiyya ne ya tabbatar da afkuwar lamarin, ya kuma kara da cewa, mahunkuntar kasar sun haramta shigo da goro zuwa kasar komai kankantarsa.
KU KARANTA: Suleiman Hashimu ya tafi aikin Hajji
Rahotanni na cewa jami’an ofishin jakadancin Najeriya a Jeddah na ta rokon hukumomin kasar da su yiwa alhajin afuwa, domin duk wanda aka kama shi da kwaya zai fuskanci hukuncin kisa ne.
Wani sakon kar-ta-kwana da wani alhaji da ke birnin Madina ya aiko Najeriya, kuma ake ta yadawa a zaurukan sada zumunta na Whatsapp a wayar hannu, ya ce jami’an kasar na caje mahajjata daya bayan daya da na’ura mai kwakwalwa a garin, don gano wanda ke dauke da kwayar magani wacce iri ce, sannan ya yi kira ga wadanda ke tahowa da cewa, kar su kuskura su taho da goro, domin a cewarsa, akwai hukuncin kisa ga duk wanda aka kama.
The post Kaicho! An kama Alhajin Nigeria da goro a Saudia appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.